NLC ta yabawa gwamnatin tarayya kan karin albashin ma’aikata a Najeriya

Kungiyar kwadago ta Kasa ta yabawa gwamnatin tarayya kan karin kaso 40m na albashin ma’aikata a kasar nan.

Rahotanni na cewa Wannan wani bangare ne na kudurori a karshen taron majalisar gudanarwa na kungiyar NLC.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta NLC, Kwamared Joe Ajaero, da babban sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja ya sanyawa hannu, wadda aka rabawa
manema labarai a ranar Alhamis.

Kungiyar ta NLC ta kuma gargadi ‘yan majalisar jihar da su daina yada labaran da gwamnonin jihohin ke yi wa ma’aikata a jihohinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *