Masu rubuta jarrabawar kimanin 60,000 sun gamu da matsaloli a cikin kwana 2 da suka wuce.

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i a Najeriya (JAMB) ta ce masu rubuta jarrabawar kimanin 60,000 ne suka gamu da matsaloli a cikin kwana biyun da suka wuce.

Adadin wani kaso ne a cikin mutum 947,000 da suka rubuta jarrabawar JAMB a wannan lokaci.

Shugaba sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana haka bayan rangadin wuraren da ake rubuta jarrabawar tare da Babban Magatakardan hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede da sauran jami’ai ranar Alhamis a Abuja.

Ya bada tabbacin cewa za a bai wa duk wanda ya yi rijista don rubuta jarrabawar JAMB damar yin hakan, yana cewa hukumar ta shawo kan matsalolin na’urorin da aka fuskanta a ranar farko ta rubuta jarrabawar a wasu cibiyoyi da ke faɗin ƙasar.

Dr Fabian Benjamin ya ce wannan ce jarrabawa mafi inganci da suka taɓa yi a tsawon shekaru, ko da yake ya san wasu za su yi jayayya da abinda ya faɗa saboda matsalolin da aka samu ranar Talata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *