Buhari ya Kara wa’adin mulkin shugaban NIS, Isah Jere

Kwanturola Tony Akuneme, jami’in hulda da jama’a na NIS ne ya bayyana hakan ga jaridar DAILY POST a ranar Juma’a.

A cewar sa, wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wasikar karin wa’adin da Buhari ya rubuta, mai dauke da rattaba hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

An yi rashin tabbas da cece-kuce game da ritayar Jere.Sabon ci gaban zai kawo jinkiri ga Sabis ɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *