Yahaya Bello ya yi nasara kan ƙarar da ya shigar da EFCC kan ƙwace masakadarorin sa.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi nasara kan ƙarar da ya shigar da hukumar hana yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), kan ƙwace masa kadarorin sa.

Rahotanni na cewa, mai shari’a Nicholar Oweibo na babbar kotun tarayya a Legas, ya yi watsi da umurnin kwace kadarori 14 na gwamna Yahaya Bello da hukumar EFCC ta samu.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar a bisa dalilin cewa ba ta da hurumin sauraron ta. Alƙalin ya bayyana cewa sashi na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya, ya ba gwamna mai ci ko shugaban ƙasa kariya daga kowace irin tuhuma.

A ranar 22 ga watan Fabrairu kotun ta bayar da umurnin ƙwacewa na wucin gadi bayan ƙarar da EFCC ta shigar tana neman kwace kadarori 14 da suke a Legas, Abuja da haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE).

Sai dai bayan wannan umurnin na kotun, gwamnan ya shigar da ƙarar jayayya da wannan hukuncin na bayar da umurnin ƙwace kadarorin, inda ya nemi da a yi watsi da shi.

Gwamnan ya ta’allaƙa ƙarar sa akan cewa kadarorin da aka lissafo, ba na kuɗin haram bane, domin ya mallake su tun kafin ya zama gwamnan jihar Kogi, saboda haka ba ta yadda za ayi ya siye si da kuɗin jihar Kogi.

Ya kuma ƙara da cewa, sashi na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya, an haramta wa EFCC shigar da ƙara akan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *