Shugaba Buhari Ya isa wurin faretin sojoji sanye da kakin soji

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa wajen bikin kaddamar da faretin sojojin Najeriya 2023.

Buhari wanda ya isa dandalin Eagle Square, inda aka gudanar da faretin, da misalin karfe 10:18 na safe ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.

Janar din sojan mai ritaya yana sanye ne da kakin soji na bikin kuma a halin yanzu yana bita ga sama da hafsoshi 1,000 da ke shirin yin faretin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor; babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Gen. Faruk Yahaya, da Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Baba ne suka halarci taron.

Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *