Gwamnati: “Babu wani dan nigeriya daya rasaransa sakamakon yakin sudan”

Gwamnatin tarayya ta bada tabbacin cewa babu wani dan nigeriya daya rasa ransa sakamakon yakin basasar da ake fama dashi a kasar sudan.

Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin cewa babu wani dan Nijeriya da ya rasa ransa sakamakon yakin basasar da ake fama da shi a kasar Sudan, ta kuma bayyana cewa tuni gwamnatin Saudiyya ta fara kwashe ‘yan Nijeriya da dama ta ruwa.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da Karamin Ministansa, Zubairu Dada ne suka bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban
kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Da yake magana kan batun da ya shafi kwashe ‘yan Nijeriya da suka makale a Sudan, Dada ya ce gwamnatin Nijeriya ta samu nasarar samun izini daga gwamnatin Sudan na kwashe ‘yan Nijeriya daga kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *