Ministan yada labarai da raya al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a jiya ya ce ‘yan kwangilar da ke aikin Hanyar Kano zuwa Zariya da Zariya zuwa Kaduna, da masu aikin gadar Neja ta biyu za su kammala nan da ranar 15 ga watan Mayu.
Ya kuma shaida wa manema labarai bayan taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya cewa za a mika babbar hanyar Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 116 ga gwamnatin tarayya a ranar 30 ga Afrilu.
Mohammed ya ce an amince da N1.398bn don sake duba kwangilar kammala aikin gadar Uto mai nisan kilomita 2.6 a Ikenke jihar Delta wanda rukuni na biyu ne, daga N4.435bn zuwa N5.835bn.
An kuma kammala gadar Loko-Oweto, haka kuma gadar Ikom itama ta kammala
Sakatariyar Gwamnatin tarayya a Nasarawa, Awka, Bayelsa da kuma jihar Zamfara an kammala su, sannan kuma aikin gina gidajen Zuba, gidaje 700, su ma an riga an fara aiki.
Ministan Noma da Raya Karkara, Muhammad Abubakar, ya ce an amince da bukatar gina helkwatar kamfanoni na ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya.
Ya ce kuma akwai karin wasu ayyukan da shugaba Buhari zai kaddamar kafin ya bar mulki, zuwa ga sabuwar gwamnati.