Babu jiha da take da damar ƙarakuɗin kujerar aikin hajji ta bana – NAHCON

Hukumai aikin Hajji ta Najeriya ta ce babu wata jiha da take da damar ƙara kuɗin kujerar aikin hajji ta bana.

Shugaban hukumar Alhazan ƙasar Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka a wajen taron shugabannin hukumar Alhazai ta jihohi da sauran hukumomi.

Alhaji Hassan ya ce duka hukumomin lhazai n jihohin ƙasar 36 sun amince da kuɗin kujerar aikin hjji da hukumar ta sanar.

Ya ƙara da cewa hukumar ta amince cewa za a fara jigilar maniyyata ranar 21 ga wtan Mayu.

Alhaji Zikrullah Hassan ya ce hukumar Alhazan za ta sake nazarin kujerun da ta ware wa kowacce jiha tare da masu ruwa da tsaki, a ranar 28 ga watan Afrilu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *