Dakarun Operation Hadarin Daji sun hallaka akalla ‘yan ta’adda biyar a wani bata-kashi da suka yi da ‘yan ta’addan a wani yanki dake jihar Zamfara.
Rahotanni na cewar, dakarun sun yi wannan aikin ne a lokacin da suke aikin sintiri a yankin Damri da karamar hukumar Bakura ta jihar.
Rahotan ya kuma bayyana cewa, sojojin sun samu bayanan sirri na gaskiya game da motsin ‘yan bindigar da tulin shanun da suka sato.
A cewar rahoto, nan take sojojin suka gaggauta daukar damara tare da taran ‘yan bindigar a kauyen Galadimai da ke lardin Damri a karamar hukumar ta Bakura.
Bayan arangamar da suka yi, an hallaka ‘yan bindiga uku nan take, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Yayinda suka kwato kayayyakin daga hannun ‘yan bindigar da suka hada da bindiga kira AK47 guda daya alburusai masu girma da kuma babura gida biyar.
Bugu da kari, sun kwato shanu, da rakuma da kuma tumaki masu tarin yawa.