EFCC zata sake tuhumar Femi Fani-Kayode da wasu mutum 3

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) zata sake tuhumar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da wasu mutum uku, a babbar kotun tarayya dake Abuja.

Rahotanni na cewar za a sake gurfanar dasu Fani-Kayode ne bisa zargin ɓarnatar da N4.6bn

Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya bayyanawa alƙalin babbar kotun tarayya ta Legas, Daniel Osiagor, cewa sake tuhumar Kayode ya zama tilas bayan kotun ɗaukaka ƙara a jihar Legas tayi watsi da tuhume-tuhumen da ake musu.

Oyedepo ya bayyana cewa duba da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar, dukkanin wasu hujjoji da takardun da suka gabatar, suna buƙatar a baiwa hukumar domin ba ta damar sake shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *