NEMA zata fara jigilar kwaso ‘ƴan Najeriya 5,500 da suka maƙale a ƙasar Sudan

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta sanar da fara jigilar kwaso ƴan Najeriya 5,500 da suka maƙale a ƙasar Sudan,a wannan rana ta talata.

A cewar daraktan ayyuka na musamman na hukumar NEMA, Mr. Onimode Bamidele, tuni har shugaban hukumar ya isa birnin Alkhahira na ƙasar Masar domin daidaita yadda za a kwaso mutanen

Bamidele ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels

A yayinda yake tabbatar da cewa shirye-shirye sun yi nisa sosai kan dawowar su, ya kuma bayyana cewa ɗalibai da sauran mutane kimanin 5,000 ne ake saran kwasowa, amma yayinda za’a fara kwaso mutune 2,500 zuwa 2,800 ciki har da iyalan ma’aikatan ofishin jakandancin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *