Karin ‘yan mata Chibok 2 sun tsere daga hannun Boko Haram

An samu ƴan mata guda biyu daga cikin ɗaliban makarantar sakandiren kwana ta Chibok a jihar Borno, da suka sake guduwa daga hannun mayaƙan ƙungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram.

Shekara 9 da suka gabata mayaƙan Boko Haram sun kutsa har cikin makarantar sakandiren inda suka yi awon gaba da ɗalibai da yawa.

Rahotanni na cewar mazauna jihar sun tabbatar da cewa ƙara tsananta luguden wuta da jami’an sojoji suke yi kan maɓoyar ƙungiyar ya sanya ƴan matan suka samu damar tserewa daga dajin Sambisa.

Wata majiya daga fannin tsaro ta bayyana sunan ɗaliban da suka tsere a matsayin Hauwa Mutah da Esther Markus.

Kawo yanzu daliban makarantar 96 ne suka rage a hannun kungiyar Boko Haram da ta sace su tun a watan Afrilun shekarar 2014.

Makonni biyu da suka gabata, rundunar sojin ta Operation Hadinkai da ke yaki da kungiyar, ta bayyana cewa akwai saura mutune 98 daga cikin Daliban Chibok a hannun kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *