JAMB ta fara gudanar da jarrabawar UTME ta shekarar 2023 a fadin Najeriya.

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta fara gudanar da jarrabawar UTME ta shekarar 2023 a fadin Nijeriya baki daya.

Jarrabawar UTME da aka fara a ranar Talata 25 ga Afrilu, za a cigaba da gudanar da ita har zuwa ranar Laraba 3 ga Mayu, 2023.

Hukumar JAMB ta bayyana cewa sama da mutane miliyan 1.6 ne suka yi rajistar UTME din ta shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *