Alkalai 257 zasu saurari kararrakin da suka taso daga zabukan 2023 a Najeriya.

Hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa NJC ta bayyana cewa alkalai 257 ne za su saurari kararrakin da suka taso daga zabukan 2023 a kasar nan.

Ana sa ran za a fara shari’ar kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da kotunan kararrakin zabe na jihohi a watan Mayu bayan hutun ranar ma’aikata.

A yanzu dai hankulan ‘yan Najeriya sun karkata zuwa kotunan saboda yadda ‘yan takarar da suka fusata a fafatawar ranar 25 ga watan Fabrairu da ta 18 ga watan Maris suka yi yunkurin neman hanyar soke nasarar da aka samu a kansu.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga duk wadanda suka yi nasara a mukamai daban-daban.

Tuni dai aka shigar da daruruwan korafe-korafe domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya da na gwamnoni da na majalisun jihohi.

Amma ana sa ran ƙarin korafe korafen, sakamakon zaɓen da aka gudanar da bai kammala ba na ranar 15 ga Afrilu a fiye da jihohi 20, bisa la’akari da tanade-tanaden Dokar Zaɓe, 2022.

Sashe na 132 (7) & (8) yana ba da damar shigar da koke koke a cikin kwanaki 21 bayan bayyana sakamako.

Wadanda ake kara suna da kwanaki 21 su amsa, yayin da kotun ke da kwanaki 180 don yanke hukunci.

An zabo manyan jami’an shari’ar da za su jagoranci sauraren korafin ne daga babbar kotun jiha, babbar kotun tarayya da kotunan ma’aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *