Alamu na nuni da cewa Buhari zai mika mulki tare da bashin tiriliyan 46.25

Alamu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga gwamnati mai jiran gado tare da bashin Naira tiriliyan 46.25.

A cewar ofishin kula da basussuka na kasa, DMO, jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya kai naira tiriliyan 46.

An ruwaito cewa, duk da illar da tuni dimbin bashin da ake bin kasar nan ya haifar , gwamnatin ta ce ta samu amincewa daga bankin duniya kan wani rancen Naira miliyan dubu dari uku da sittin da tara gabanin cire tallafin man fetur a watan Yunin wannan
shekarar ta 2023.

A cikin shekaru takwas na gwamnatin Buhari, bashin Najeriya ya karu daga Naira tiriliyan 12.6 a shekarar 2015 zuwa sama da Naira tiriliyan 46 a shekarar 2023.

Lamarin dai na ci gaba da dagula al’amura a kasafin kudi, musamman yadda asusun lamuni na duniya, IMF, ya ce Najeriya ta kusan kwashe baitul-malinta wajen biyan basussuka a shekarar 2022.

Hukumar tara haraji ta kasa ta ce ta tara Naira tiriliyan 10 a cikin kudaden shiga a shekarar 2022, inda kasafin kudin 2023 ya kai Naira tiriliyan 21.83 tare da wawakeken gibin Naira tiriliyan 11.34.

A kan haka, babban aikin da ke gaban kalubalen tattalin arzikin kasar nan zai kasance ne a karkashin zababben shugaban kasa mai jiran gado bayan rantsar da shi a ranar 29 ga
watan Mayu, 2023.

Sai dai masana tattalin arziki sun ce gyara tattalin arzikin Najeriyar da ke fama da basussuka zai kasance abu mai matukar wahala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *