“Aikin shimfida bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano ya kai kashi 70” – NNPC

Kamfanin mai na Najeriya (NNPC) ya ce aikin shimfida bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) ya kai kashi 70 cikin 100.

Babban jami’in kamfanin na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana hakan a yayin wani rangadin da ya kai daya daga cikin wuraren da ake gudanar da ayyukan da ke garin Ahoko na jihar Kogi.

NNPCL ya ce aikin bututun iskar gas da tashoshi da ake kira da AKK wani shiri ne da zai kara karfafa alaka tsakanin yankin arewacin kasar nan da yankin Neja Delta da sauran sassan Najeriya.

Bututun na iya jigilar iskar gas sama da lita tiriliyan biyar a kowace rana zuwa kamfanonin samar da wutar lantarki masu zaman kansu guda uku (3) da ake shirin samarwa a Abuja, da Kaduna, da Kano, da sauran masana’antu masu amfani da iskar gas.

Aikin, a cewar NNPCL, yana da damar inganta karfin samar da wutar lantarki na kasa da kuma tattalin arzikin kasa baki daya ta hanyar samar da masana’antu da kuma sauran hanyoyi na bunkasar tattalin arziki.

Tun bayan kaddamar da aikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a watan Yunin shekarar 2020, kamfanin NNPC ya ce ya samu gagarumar nasara kuma aikin ya yi nisa wajen aiwatar da shi a kan kari.

Da yake magana a ranar Litinin din da ta gabata, Mista Kyari ya ce ya zuwa yanzu kamfanin NNPC ya fitar da dala miliyan dubu 1 da dari 1 domin gudanar da aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *