Sarkin Zuru ya yi kira da a tabbatar an kama wadanda keda hannu wajen “cin zarafin” Farfesa Abdullahi Abdul Zuru

Mai Martaba Sarkin Zuru, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami Mai ritaya, ya yi kira da a tabbatar an kama tare da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen “cin zarafin” Farfesa Abdullahi Abdul Zuru a jihar Adamawa.

Wasu ’yan daba ne dai suka kai wa Zuru hari a jihar Adamawa a ranar 17 ga watan Afrilu a lokacin da yake bakin aikin hukumar zabe ta kasa (INEC) a matsayin kwamishinan kasa daga yankin Arewa maso Yamma
da aka tura jihar domin gudanar da zaben gwamna.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Sarkin ya bayyana harin da aka kai wa Zuru a matsayin mafi girman rashin mutuntawa da kuma wulakanta wani dan Najeriya da ke gudanar da aikinsa bisa doka da oda.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya da su kara kaimi wajen kamo bata garin, yana mai cewa matakin da ‘yan ta’addan suka dauka yana da ban tsoro kuma bai kamata kyale batun hakanan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *