NBS: “Yawan masu amfani da intanet a Najeriya sun karu zuwa miliyan 154”.

Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa yawan masu amfani da intanet a kasar nan ya karu zuwa miliyan dari da hamsin da hudu a zango na hudu na shekarar 2022.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin sabbin alkaluma da ta fitar inda alkaluman sun nuna yawan masu amfanin ya karu da kashi tara da digo bakwai cikin ɗari daga mutum miliyan dari da arba’in da daya da dubu dari tara a karshen zangon shekarar 2021.

Hukumar ta kara da cewa, adadin masu kiran waya ma ya karu zuwa miliyan dari biyu da ashirin da biyu da dubu dari biyar daga mutum miliyan dari da casa’in da biyar da dubu dari hudu da sittin da uku da
alkaluma suka nuna na 2021, wanda haka ke nuna karuwar da kashi sha uku da digo takwas da bakwai cikin dari.

Wannan ya nuna cewa, yawan masu kiran wayan ya yi ta karuwa da kashi hudu da digo takwar da tara bisa dari a duk karshen zango a shekarar da ta gabata.

Alkaluman na NBS sun bayyana “Legas a matsayin jihar da ta kowacce yawan masu kiran waya, inda ta ke da mutum miliyan ashirin da shida da dubu dari hudu da sittin da dari takwasa da saba’in da bakwai, yayin da jihar Bayelsa ta zo ta karshe da mutum miliyan daya da dubu dari biyar da saba;in da daya da dari shida da casa’in da biyu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *