MDCAN ta bukaci Tinubu, daya tunkari kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya da zarar yahau mulki

Kungiyar kwararrun likitoci masu kula da lafiyar hakori ta Najeriya (MDCAN) ta bukaci zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya tunkari kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya da zarar ya hau mulki a watan Mayu.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin sakon taya murna mai dauke da sa hannun shugabanta, Dr Victor Makanjuola da Sakatare Janar, Dr Yemi R. Raji.

Kungiyar ta ce za a bukaci kulawar gaggawa daga sabuwar gwamnati mai shigowa kan duk wata matsala da ta ke ci wa al”umma tuwo a kwarya musamman abinda ya shafi kula da lafiya.

Ta ce ta himmatu wajen aiwatar da dokokin da suka shafi kiwon lafiya kamar Dokar Kiwon Lafiya ta 2014 da kuma Dokar Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) ta 2022 a kokarinta na cike gibin kudaden da ake
bukata don fadada hanyoyin samun kulawa da yawancin ‘yan Najeriya ke bukata zuwa ga cimma babban tsari na Kula da Lafiya a Duniya.

Kwararrun likitocin sun ce suna sa ran ganin wa’adin Tinubu ya kawo cigaban zamani a fannin kiwon lafiya har ma da sauran bangarori da ke bukatar kulawar gaggawa a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *