Gwamnatin tarayya za ta fara kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan

Gwamnatin tarayya tace za ta fara kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan mai fama da rikici cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta fara kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan mai fama da rikici cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Rahotanni sun nunar da cewa rikici tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke ba da umarni ga dakarun (RSF),
ya wargaza kasar.

Daruruwan mutane ne aka kashe tun bayan barkewar rikicin a ranar Asabar din makon da ya gabata a babban birnin kasar Sudan tsakanin dakarun janar-janar dinguda biyu.

Dubban ‘yan Najeriya ne a kasar Sudan inda 5,500 daga cikinsu suka nuna sha’awar a kwashe su zuwa gida Najeriya.

Ministan ya yi watsi da ikirarin da wasu ke yi na cewa gwamnatin tarayya ba ta nuna damuwa sosai kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki a kasar ta Sudan mai fama da rikici.

Ya kara da cewa hukumomin gwamnati na kokarin ganin an kai dauki ga wadanda suka makale.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *