Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun fara sukar shirin gwamnatin tarayya na rage radadin janye tallafin man fetur.
Shirin wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi ya ciwo bashin dala miliyan 800 domin raba wa marassa galihu da sunan rage radadin cire tallafin mai.
Sanata Aliyu Ndume da ke wakiltar mazabar Borno ta kudu yana daya daga cikin ‘yan majalisar da ke ganin kudin rage radadin ba za su kai ga marassa karfi ba.
Dan majalisar ya ce kudin sun yi kadan idan aka dubi yawan ‘yan Najeriya da ke fama da talauci.
Sanatan ya dora ayar tambaya kan yadda kudin za su amfani talakawa idan aka dubi yawansu da kuma yadda za a raba su.
Ndume ya ce bai ga hanyar da za a bi wajen zabo talakawa miliyan 50
daga cikin mutane sama da miliyan 200 da Najeriya ke da su ba cikin
sauki.
Sanata Ndume ya kara da cewa komai talaucin mutum idon a ka bashi
11,840 ba wani taimako a ka yi masa ba saboda ko rabin buhun
shinkafa kudin ba za su saya ba.
Dan majalisar ya bayar da shawara kan abin da ya kamata gwamnati ta
yi da kudin domin su amfani talakawa a lungu da sakon Najeriya.
Har’ilayau, ya ce za a iya amfani da kudin wajen gyara makarantu a
kananan hukumomin Najeriya.