Rasha ta kori jami’an diplomasiyyar Jamus da ke ƙasarta.

A yayin da dangantaka tsakanin Rasha da ƙasashen yamma ke ci gaba da yin tsami saboda yaƙin Ukraine, Rasha ta ɗauki matakin korar wasu jami’an diplomasiyyar Jamus da ke ƙasarta.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova a ranar Asabar na cewa matakin ramuwar gayya ne kan matakin da Jamus ɗin ta ɗauka
na korar ma’aikatan ofishin jakadancin Rasha Jamus.

Kafar yaɗa labaran RIA News Channel, ta ce Jamus ta kori fiye da ma’aikatan ofishin jakadancin Rasha da ke Jamus.

Wani jami’i a ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen Jamus ya ce ƙasarsa ta kwashe kusan makonni tana tattaunawa da Rasha kan batun.

Matakin da Rasha ta ɗauka na korar jami’an diplomasiyyar na Jamus shi ne na baya-bayan nan a jerin korar jami’an diplomasiyyar ƙasashen yamma, tun bayan mamayar Ukraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *