APC mai mulkin kasa ta rushe kwamitin da ta kafa a bara na yaƙin neman zaɓen shugaban a zaɓen 2023.
Cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta fitar a ranar Asabar, tsakanin Babban Daraktan APC gwamna Simon Bako Lalong da kuma Sakataren kwamitin James Abiodun Falake.
Jam’iyyar ta yi godiya a madadin shugaban yaƙin neman zaɓen 2023 Muhammadu Buhari, ga duka mutanen da suka taimaka aka kai ga nasarar da aka samu.