Zababben Dan Majalisa, Ismaila Maihanci Ya Rasu

Zababben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Jalingo/Yorro/Zing na Jihar Taraba,  Ismaila Maihanci, ya rasu kwana 37 kafin rantsarwa.

Isma’il mai shekara 36 a duniya ya rasu ne a safiyar Asabar, washegarin karamar Sallah, inda ake sa ran gudanar da jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.

Zababben dan majalisar, karkashin jam’iyyar PDP, ya kasance tsohon sakataren jam’iyyar na Jihar Taraba.

Dan kasuwa ne kuma ya taba zama mai ba da shawara na musamman ga gwamnan jihar, Darius Ishaku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *