Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa, Hudu Yunus Ari, ya yi layar zana tun bayan da ya sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar ta barauniyar hanya.
Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Barista Festus Okoye, ya ce tun bayan da Barista Hudu Yunus Ari ya sanar da haramtaccen sakamakon zaben, ya daina
amsa waya.
Okoye ya ce kawo yanzu INEC ba ta san inda Barista Hudu ya shige ba, kuma bai kai kansa domin amsa tambayoyi a hedikwatar hukumar kamar yadda ta umarce shi ba.
Okoye ya bayyana haka ne a wata hirar talabijin da aka yi da shi ranar Juma’a, inda ya ce idan binciken ’yan sanda ya ga cewa ya kamata, za su iya bayyana Hudu a matsayin mutumin da ake nema
ruwa a jallo.
Tuni dai INEC da Shugaba Buhari sun umarci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da ya tsare Hudu ya bincike shi domin gurfanar da shi a gaban kotu kan gaban kansa da ya yi wajen sanar da sakamakon gwamnan jihar Adamawa ba bisa ka’ida ba.
A ranar Lahadi ne Barista Hudu ya sanar da sakamakon alhali ba a karbi sakamakon zaben karanan hukumomi 11 ba a zaben da aka karasa a ranar Asabar.
Barista Hudu ya yi wa Jami’in Tattar Sakamkon Zaben, Farfesa Mohammed Mele, shigar sauri wajen sanar da haramtaccen sakamakon ne awa guda kafin lokacin da aka sanya na ci gaba da tattara alkalaman zaben.
Sai dai ba a jima ba, INEC ta sanar cewa sanawar tasa ta saba doka kuma ba ta da tasiri, hasali ma ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zaben, aikin Farfesa Mele ne.
A nan ne ta dakatar da aikin tattara sakamakon zaben, ta gayyaci Hudu da Mele da jam’iyyun da suka shiga zaben da sauran masu ruwa da tsaki zuwa hedikwatarta da ke Abuja domin yi wa tufkar hanci.
An cikin haka ne Binani, wadda har ta yi jawabin godiyar samun nasara, ta je kotu tana neman a hana INEC sauya sakamakon Hudu ya sanar, amma kotu ta yi watsi da bukatar.