Gwamnatin Najeriya Ta Fara Biyan Bashin Karin Albashi Ga Ma’aikata

Gwamnatin tarayya ta fara biyan bashin kashi 40 cikin 100 na karin albashi ga ma’aikatan gwamnati, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito a ranar Asabar.

Wakilinmu da ya zanta da wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya a ranar Asabar din da ta gabata ya gano cewa ma’aikatan sun fara karbar sanarwar basussukan daga bankuna a ranar Asabar 22 ga watan Afrilu, 2023.

Wani babban ma’aikacin gwamnati wanda ya zanta da wakilinmu a boye a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ya lura cewa basussukan sun zo ne tare da albashin watan Afrilun 2023.

“Na karbi bashin kaina a yau. Wasu daga cikin abokan aikin mu ma sun tabbatar da karbar basussukan su. Ya shigo tare da albashinmu na watan Afrilu.”

Wani ma’aikacin gwamnati da ya tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar tattaunawa da wakilinmu a Ibadan ya ce, “Eh gaskiya ne. Ko da yake ni malami ne da ke makarantar Gwamnatin Tarayya, zan iya tabbatar muku cewa na karɓi albashin Afrilu 2023 tare da bashin da nake bi.”

Idan za’a iya tunawa mun ta ruwaito cewa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta bayar da shawarar kara albashin ma’aikata kashi 40 cikin 100 domin dakile illolin da shirin cire tallafin man fetur da ake shirin yi.

Kakakin Ma’aikatar Kwadago,da samar da Ayyukan yi, Olajide Oshundun, wanda ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa karin kudin zai shafi dukkan ma’aikata daga mataki na 1 zuwa na 17.

A farkon watan Maris ne Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashin ma’aikatan kasar nan.

Ya kara da cewa karin albashin an saka shi a cikin kasafin kudin shekarar 2023, inda ya ce zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2023.

Ngige ya bayyana karin albashin a matsayin alawus na musamman ga ma’aikatan gwamnati bisa la’akari da halin da ake ciki a fannin tattalin arziki da nufin taimakawa ma’aikatan gwamnati wajen rage radadin hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa, karin kudin sufuri, farashin gidaje da wutar lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *