Gwamnati: Ba za mu iya kwaso daliban Najeriya dake karatu akasar Sudan a halin yanzu ba.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za a iya kwaso daliban Najeriya da ke karatu a kasar Sudan a halin yanzu ba.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a yayin da daliban Najeriya da ke karatu a Sudan su ka roke ta da dawo da su gida, bayan kazamin fada ya barke a kasar.

Wata sanarwa da shugabar hukumar kula da ‘yan nigeria da ke kasashen ketare wato Abike Dabiri Erewa, ta fitar a shafin Twitter, ta ce akwai yiwuwar duk jirgin da ya sauka a kasar a banka masa wuta a kona shi.

A cewar Dabiri, a jiya Juma’a, an kona duka jiragen da ke filin tashin jirage na Khartoum kuma an saka dokar hana zirga-zirga.

Kimanin mako biyu ke nan ana gwabza fada a kasar tsakanin wasu bangarori biyu da ke rikici da juna kan shugabancin kasar.

Rikicin bangarorin biyu da ke goyon bayan wasu janar-janar na soja kan shugabancin kasar, ya yi ajali da kuma jikkata daruruwan mutane.

Lamarin dai ya kai ga kasashen duniya sun yi kira ga bangaorin da su kai
zuciya nesa.
An yi luguden wutan ne a ranar Juma’a da ake bikin Karamar Sallah, ranar
da bangarorin su ka amince su tsagaita wuta na kwana uku domin ba wa
’yan kasar damar yin bukukuwan Karamar Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *