A shirye nake na koma Nijar da zama idan na sauka daga mulki – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake ya koma kasar Jamhuriyar Nijar da zama idan ya sauka daga mulki.

Buhari ya sanar a ranar Karamar Sallah cewa ya kosa ya bar mulki ya koma mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina, koda ya ke ya ce a Daura ma, idan ya koma can su ka dame shi, to sai ya tsallaka ya
koma kasar Nijar.

Ya ce tuni ya riga ya hada kayansa domin kuwa, ya kudirin aniyar zama nesa da Abuja idan ya sauka daga mulki.

Buhari wanda ya jima da cewa ya kosa ya bar mulki ya ce komawarsa Daura zai sama mishi isasshen hutu nesa da Abuja, bayan shekarun da ya yi a bisa mulki.

Hakan kuma, a cewarsa, zai kuma ba wa shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, damar yanke shawara da gudanar da mulkinsa yadda yake so.

Buhari ya kuma yaba wa ’yan Najeriya bisa hakurinsu da kamun ludayin gwamnatinsa na tsawon shekaru takwas.

Ya kara da cewa ya dauki laifin duk wani laifi ko caccaka ko zargin da ake wa gwamnatinsa, saboda shugabanci ya gaji haka.

Sannan ya roki ’yan kasar da su yafe masa duk abin da ya yi musu ba daidai ba a tsawon shekarun mulkinsa.

Da yake karbar bakuncin mazauna birnin tarayya da suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, Buhari ya ce shirme ne yadda ’yan siyasa suka rika amfani da
bambancin addini da kabilanci a matsayin makaman siyasa a zaben da ya gabata.

Ya ba da misali da cewa a duk shari’o’in da ya shigar Musulmai ’yan Arewa shugabannin Kotun Koli a lokacin, amma hakan bai sa ya yi nasara a kotu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *