Sarkin musulmi ya bukaci alummar Nigeriya da su yi addu’ar miƙa mulki gasabuwar gwamnati cikin lumana

Mai alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na 3 ya bukaci alummar Nigeriya da su yi addu’ar miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana a faɗin ƙasar nan.

Sarkin musulmin ya yi wannan kiran a wata sanarwa da babban sakataren ƙungiyar Jama’atu Nasir Islam (JNI), Dr Khalid Aliyu, ya fitar a Kaduna.

Sarkin musulmin kuma shugaban JNI, ya kuma yi fatan ƙarewar wa’adin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari cikin kwanciyar hankali inda ya yi kira ga gwamnatocin da za su karɓi madafun iko da su yi gaskiya, adalci da kuma buɗe kunnuwan su, musamman kan lamuran tsaro da kuma tsoron Allah wajen gudanar da mulkin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *