NCOS: “Akwai akalla fursunoni 3,298 da aka yanke wa hukuncin kisa”

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta ce akwai akalla fursunoni 3,298 da aka yanke wa hukuncin kisa kuma suke zaman jiran a zartar musu da shi a gidajen kurkukun kasar.

Kakakin hukumar na kasa, Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Laraba a Abuja.

Ya ce galibi a Najeriya ba a cika zartar da hukuncin ba ga wadanda aka yanke musu ba.

Ya ce, Akwai lokutan rashin tabbas yayin da wadanda aka yanke wa hukuncin suke daukaka kara zuwa kotuna na gaba.

Fursunonin da ke jiran hukuncin kisa wasu daga cikinsu kan shafe kusan shekara 15 bayan yanke musu hukuncin.

Ya ce da yawa daga cikin irin wadannan fursunonin sun aikata munanan laifuka ne irin su kisan kai, fashi da makami da ta’addanci da dai sauransu.

Sai dai ya ce a baya, an sami nasarar zaratr da hukuncin kisan ga mutane da dama, kafin kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan Adam su dada yin yawa sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *