Ana fargabar mutum biyu sun mutu bayan da wani ginin da ba a ƙarasa ba ya faɗi a Abuja babban birnin Najeriya.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba a kan titin Ademola Adetokunbo Crescent, da ke unguwar Wuse 2 a tsakiyar birnin.
Rahotanni sun ce an kuɓutar da ma’aikata huɗu da ransu, inda mutum biyu suka samu munanan raunuka yayin da ake ci gaba da aikin ceton.
Ana aikin ceton ne tsakanin haɗin gwiwwar jami’an bayar da agajin gaggawa, da jami’an kashe gobara, da jami’an Civil Defence, da ‘yan sanda da sauran masu sa-kai.
Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa na FEMA , Abbas Idris ya shaida wa manema labarai cewa ”mutum biyu sun samu munanan raunuka,” yana mai cewa likitoci ne kawai za su tabbatar da mutuwarsu.