Hukumar kula da rarraba hasken wutar lantarki ta kasa tace nan bada dadewa zata samar da mitoci miliyan hudu da aka riga aka biya ga masu amfani da wutar lantarki a kasar nan.
Rahotanni na cewar Aisha Mahmud, Kwamishiniyar hukumar mai kula da harkokin masu amfani da lantarkin, ita ce ta bayyana hakan a wajen taronN warware korafe-korafen kwastomomi da aka gudanar a birnin Jos na jihar plato.
Aisha Mahmud, wadda ta bayyana karancin mitocin a kasarnan a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin da hukumar ke fuskanta a halin yanzu, tayi nuni da cewar nan bada dadewa ba kalubalen zai zama tarihi.
Ta kara da cewar an samar da hanyoyin samar da mitocin ne ta hanyar Hukumar Kula da Matsalolin Jama’a ta gwamnatin tarayya.
Kazalika ta danganta hauhawar farashin wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki, da tsadar iskar gas,da samar da ma’aikata, da sauran abubuwan da suka shafi tattalin arziki a kasar nan da cewar nan gaba kadan zai zama tarihi