IGP ya kaddamar da rukunin gidaje 88 a barikin ‘yan sanda a Kano

Babbban sufetan ‘yan sandan kasarnan Usman Alkali Baba ya kaddamar da rukunin gidaje 11 na gidaje masu daki biyu wadanda suka kunshi gidaje 88 a barikin yan sanda na bompai a Kano

Ya kuma yiwa jami’an rundunar yan sandan jihar kano alkawarin cewar ana cigaban da samar da jin dadinsu domin inganta ayyukan rundunar.

Akali Baba wanda ya samu wakilcin kwamishinan yan sandan jihar kano Mamman Dauda yace rundunar yan sandan najeriya tare da hadin gwiwar wani kamfani ne suka gina gidajen.

Kwamishinan yan sandan yayi ritaya daga aikin yan sanda bayan daya cika shekaru 60 a rayuwa kamar yadda yake a kaidar aiki a kasarnan

A karshe yayi kira ga jami’an daza suci gajiyar wadannan tsare tsare da akayi domin jin dadinsu su kuma mayar da hankali wajen jajircewa da adaukar da kai kan ayyukan da aka basu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *