Gwamnatin tarayya tana shirin kaddamar da magance matsalar tsaro nan da shekaru 5

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kaddamar da magance matsalar tsaro a najeriya nan da tsawon shekaru 5

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana kaddamar da shirin na tsawon shekaru biyar ga ma’aikatar ayyuka da hukumomin tsaron dake ƙarƙashin Ma’aikatar don magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar Afonja Fatai Ajibola ya fitar, Ministan ya ce ma’aikatar harkokin cikin gida nada matukar muhimmanci ga tsaron kasa da ci gaban kasa.

Ya ce za a cimma wannan matsaya ne ta hanyoyi guda hudu da suka hadarda hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) dake sa ido kan shigowa da fita akan iyakokin kasar nan, tare da tabbatar da cewar an
kiyaye wadanda zasu cutar da ‘yan Nijeriya da jin dadin su daga waje.

Ministan ya ci gaba da cewa, hukumar tsaro ta farin kaya tana baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai wajen yaki da miyagun laifuka da tattara bayanan sirri, yayinda hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ke tsare da wadanda aka yanke musu hukunci bisa ka’ida ko kuma
suna jiran shari’a.

Yayinda yake bayyana rawar da jami’an tsaro ke takawa wajen tabbatar da tsaron kasa, Ministan ya kuma ce hukumar kashe gobara ta tarayya tana bada agajin gaggawa ga gobara da sauran abubuwan gaggawa, sannan ya kara da cewa wani sashe a ma’aikatar na yin rijistar aure da kuma tsara kasancewar baki a Najeriya.

Tunda farko anasa jawabin babban sakataren ma’aikatar Dr. Shu’aib Belgore ya bayyana cewa, rahotanni da suke samu sun nuna cewa ma’aikatar harkokin cikin gida ta gudanar da ayyukanta ba tare da wani shiri
ba har zuwa yanzu.

Dokta Belgore ya kara da cewar a yanzu Najeriya nada damar inganta gine-
ginen tsaro ta hanyar tsare-tsare na ma’aikatar harkokin cikin gida, wanda

aka samar da hadin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *