Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa Isah Jere Idris ritaya.
Hakan ya biyo bayan cikar wa’adinsa na aiki. Cikin wata sanarwa da sakataren hukumar, Obasi Edozie Edmond ya sanyawa hannu bisa umarnin ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola.
An umarci Jere daya miki ragamar aikinsa ga jami’i mafi girman mukami a hukumar.
Idan dai za’a iya tunawa an nada Isah Jere Idris a matsayin mukaddashin hukumar kafin ya yi ritaya a watan Afrilun 2022 yayinda ya samu karin wa’adin shekara daya kafin cikar wa’adinsa.
Tsawaita wa’adin zai kare a ranar 24 ga Afrilu, 2023.