An kama wani mai POS kan zarginsa da kashe miliyan 280 da aka tura masa bisa kuskure

An kama wani ma’aikacin PoS mai suna Alfa Rafiu a bisa zarginsa da almubazzaranci wajen Naira miliyan 280 da aka aika a asusun sa bisa kuskure. Wanda ake zargin.

An kama wani mai POS mai suna Alfa Rafiu a jihar Kwara bisa zarginsa da almubazzarancin kashe Naira miliyan 280 da aka tura a asusun sa bisa kuskure.

Rahma ta tattaro cewa Wanda ake zargin, mazaunin unguwar Akuji ne da ke unguwar Abayawo a karamar hukumar Ilorin ta yamma.

A cewar majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin, ba zato ba tsammani Rafiu ya yi ta kashe kudi bayan da ya samu sanarwar a cikin wayarsa na shigowar miliyoyi da dama makonnin da suka gabata.

“Kusan makonni biyu da suka gabata, ya samu sanarwar banki da dama da suka kai Naira miliyan 280 wadanda bai san komai ba.

“Amma maimakon ya jawo hankalin bankin da ya karkatar da makudan kudade cikin kuskure, sai ya yi gudu.

“Rafiu ya sayi gidaje da motoci da daukar nauyin mutane zuwa Hajji. Wasu daga cikin wadanda ya dauki nauyinsu a halin yanzu suna Saudiyya kamar yadda muke magana.

Majiyar ta kara da cewa “Ko da yake ya kasance mai kyauta ga mutane da yawa a cikin al’umma, wasu mazauna garin sun yi mamakin dukiyarsa ta kwatsam a matsayinsa na mai PoS,” in ji majiyar.

An tattaro cewa ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin daga ofishin ‘yan sanda na “C” Division, Oja-Oba, Ilorin, tare da rakiyar wasu jami’an bankin.

Lokacin da Jaridar Daily trust ta ziyarci gidansa a ranar Talata, an rufe shagon sa na PoS, kuma wasu mazauna gidan sun ce ya yi tafiya ne bai san lokacin da zai dawo ba.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi (SP), ya tabbatar da faruwar lamarin.

Eh, maganar gaskiya ce, amma hukumar binciken manyan laifuka (FCIID) ce ta kama shi daga Alagbon-Close, da ke Ikoyi, a Legas wanda hakan ya sa lamarin ya fita daga hannunmu,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *