JAMB ta tsawaita lokacin yin rajista ga daliban da ke neman gurabun karatu kai-tsaye da mako 1

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta tsawaita lokacin yin rajista ga daliban da ke neman gurabun karatu kai-tsaye da mako guda.

JAMB ta tsawaita lokacin rajistar DE ne daga ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu, da ta shirya rufewa da farko, zuwa ranar Juma’a 27 ga watan.

Mai magana da yawun hukumar JAMB, Farfesa Fabian Benjamin yace karin lokacin zai ba da dama ga dalibai masu takardar shaidar jarawabar “Cambridge A/Level daba suyi rajista ba saboda matsalar tantance takardunsu a baya su samu damar yin rajistar.

Ya ce domin saukake tantance takardun Cambridge A/Level, JAMB na aiki tare da Cibiyar Raya Al’adun Kasar Birtaniya wadda za ta samar da shafin da JAMB za ta yi amfani da shi kai-tsaye wajen tantance takardun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *