Gwamnatin tarayya ta amince a fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya

Gwamnatin tarayya ta amince a fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya wanda Jami’ar Oxford da ke Birtaniya ta samar.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ce ta ba da izinin amfanin da riga-kafin mai suna R21, duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba su kammala bincike kan rashin hadarinsa ga dan Adam ba.
Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, itace ta bayyana hakan Tace adan haka Najeriya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afirka da ta amince da riga-kafin, bayan kasar Ghana.

Sai dai duk da haka Shugabar NAFDAC din ta jaddada muhimmancin kammala binciken da ake gudanarwa a Najeriya kan riga-kafin cutar.

Cutar Maleriya wadda cizon sauro ke haifarwa na kashe sama da mutum dubu dari shida a duk shekara, akasarinsu kananan yara da mata ne a nahiyar Afirka, in ji WHO.

Rahoton WHO ya nuna a shekarar 2021 Najeriya ce kasar da ke dauke da kashi 27% na masu maleriya da kuma kashi 32% na wadanda ta yi sanadin mutuwarsu a duniya.

Izuwa yanzu dai babu tabbacin lokacin da za a fara amfani da riga-kafin R21 a Najeriya da Ghana, kuma har yanzu hukumomin duniya, ciki har da WHO na ci gaba da bincike kan nagartarsa da amincinsa ga jikin dan Adam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *