Ma’aikatan fannin sufurin jiragen sama zasu fara yajin aiki yau

Yau Litinin ma’aikatan fannin sufurin jiragen sama a kasarnan za su fara yajin aikin kwanaki biyu, domin neman a kyautata musu yanayin aiki da kuma wasu kudade da suke bin gwamnati..

An samu tsaiko a ɓangaren zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya inda fasinjoji da dama suka yi cirko-cirko bayan ƙungiyoyin ma’aikatin filin jirgin sama sun shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa mambobin ƙungiyoyin sun rufe ƙofar shiga ɓangaren tashin jiragen cikin gida na filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, wanda hakan ya sanya fasinjoji
da dama cirko-cirko.

Hakan ya biyo bayan rashin samun mafita da aka yi a taron da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa ta yi da ƙungiyoyin inda suka toge sai sun shiga yajin aikin.

Darekta Janar na hukumar hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama , Capt. Musa Nuhu shine ya kira taron domin ba ƙungiyoyin baki sun janye yajin aikin gargaɗi na kwana biyu da suka shirya shiga.

Ƙungiyoyin suna neman buƙatu da yawa daga ciki akwai, dakatar da shirin rushe hedikwatar a Legas da kuma da kiran a aiwatar da yarjejeniyar kula da jindadin ma’aikata da aka cimma da hukumar.

Jami’an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da sojoji suna a filin jirgin yayin da ƙungiyoyin suke rera waƙoƙin nuna haɗin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *