INEC za ta yi taron gaggawa a yau Litinin

Hukumar Zabe ta Kasa INEC za ta yi taron gaggawa a yau Litinin kan dambarwar da ta dabaibaye tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa.

Tun a ranar Lahadi INEC ta umarci duk jami’anta da ke lura da zaben gwamna a Adamawa, da su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan INEC ta bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaben gwamna da aka karasa a ranar Asabar.

Rahoton ya kara da cewa tun ana tsaka da tattara sakamakon zaben ne Kwamishinan INEC na Adamawa, Barista Hudu Ari, ya ayyana ’yar takarar gwamnan ta jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta yi nasara.

Lamarin da ya sanya cikin wata sanarwar gaggawa da babban jami’inta kan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zabe na Jihar Adamawa ya dauka na sanar da wanda ya lashe zaben haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi
amfani da shi ba.

Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa ba.

Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaben gwamnan Jihar Adamawa ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *