INEC ta dakatar da kwamishinan zaben Adamawa

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta umarci Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus, ya tattara nasa ya bar ofishinsa da ma harabar ofishin nan take.

Hedikwatar INEC da ke Abuja ta umarce shi kada ya kara kusantan harabar ofishin hukumar har sai abin da hali ya yi, sannan ta umarci Sakataren Gudanarwa na Jihar ya karbi ragamar ofishin

Sanarwar da Sakatariyar INEC ta Kasa, Rose Oriaran-Anthony, ta aike wa REC din wasikar ce washegarin da ya haifar da rudani ta hanyar yin riga-malam-masallaci wajen sanar da Sanata Aisha Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar.

Ya yi sanarwar ce gabanin lokacin da za a ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka karasa a ranar Asabar.

Sai dai daga bisani hedikwatar INEC ta kasa ta ce sanarwar tasa ba ta amfani ballantanta tasiri a doka, hasali ma ba shi da hurumin sanar da sakamakon zabe, domin aikin jami’in tattara sakamkon zabe ne.

Sanarwar da Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da kan Jama’a, Barista Okoye, ya fitar ta kuma dakatar da tattara sakamakon zaben sannan ta bukaci REC Hudu da baturen zaben da wakilan jam’iyyu da sauransu su bayyana a hadikwatar hukumar a ranar Litinin domin lalubo bakin zaren.

Lamarin dai ya haifar da hatsaniya, a yayin da Binani ta gabatar da jawabin nasarar cin zabe, shi kuma abokin karawarta, Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu su ga irin matakin da INEC za ta yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *