Yau Lahadi za a cigaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jiharAdamawa da aka kammala jiya Asabar.

Yayin da ake ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen gwamna da aka kammala a jihar Adamawa, an jibge jami’an tsaro a wurin da ake bayyana sakamakon zaben a Yola, babban birnin jihar.

A cibiyar ce ake sa ran sanar da sakamakon zaɓen a yau Lahadi. An ɗage bayyana sakamkon zaɓen da daddare a ranar Asabar, inda babban jami’in bayyana sakamakon zaɓe na jihar ya sanar cewa za a ci
gaba da ƙarfe 11 na safiyar yau Lahadi.

Al’ummar jihar dai na nan suna dakon sakamakon, kamar sauran al’ummun wasu jihohin da aka gudanar da zaɓen na ranar Asabar 15, ga watan Afurilu.

An gudanar da zaɓen ne a rumfunan zaɓe 67, inda aka kasa kammala zaɓe na ranar 18 ga watan Maris, wanda a sanadiyyar haka ne INEC ta ce zaɓen bai kammala ba.

A sakamakon zaɓen 18 ga watan Maris da INEC ta bayyana, gwamna mai ci na jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri ne ke kan gaba da ƙuri’a 421,524, yayin da Sanata A’isha Dahiru Binani ta jam’iyyar APC ta
samu ƙuri’a 390,275.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *