INEC ta yi watsi da sanarwar da ta ayyana Binani a matsayin zababben gwamna

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi watsi da sanarwar da ta ayyana Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna a jihar Adamawa.

Hukumar zaben ta kuma gayyaci kwamishinan zabe na jihar Barista Hudu Yunusa kan wannan furuci mai cike da cece-kuce.

INEC ta bayyana hakan ne ta shafinta na Twitter a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce, “An jawo hankalin mu ga sanarwar da hukumar zabe ta kasa ta yi na bayana sakamakon zaben gwamnan Adamawa wanda ko kammala tattara sakamakon ba a yi ba.

Don haka mun dakatar da tattara sakamakon zaben cike gurbi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *