INEC ta dakatar da aikin tattara sakamakon zaɓen gwamna a Adamawa.

Hukumar INEC ta gayyaci duka jami’anta da ke lura da zaben gwamna a jihar Adamawa, su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.

Ta kuma bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa.

A cikin wata sanarwa da babban jami’inta kan yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na ƙasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa – REC ya ɗauka na sanar da wanda ya lashe zaɓe haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *