Yahaya Bello ya bayyana Usman Ododo a matsayin dan takararsa.

A yayin da Hukumar Zabe ta Kasa ta sanya 11 ga watan Nuwamba a matsayin ranar zaben Gwamnan Kogi, Gwamna Yahaya Bello na jihar ya bayyana wanda yake so ya gaje shi.

Sai dai Yahaya Bello ya shammaci jama’a, domin kuwa dan takarar nasa ba mataimakinsa, Edward Onoja ba ne.

Da farko an yi zaton Onoja ne zai zama dan takarar Yahaya Bello, a matsayin Onojan na dan lelensa.

Edward Onoja ya kasance tsohon shugaban ma’aikatan Yahaya Bello, daga baya gwamnan ya daga likafarsa zuwa matsayin mataimakin gwamna bayan an shige Achuba a 2019.

A wani taron masu ruwa da tsaki da masu neman takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar APC suka gudanar a daren Alhamis, Gwamna Yahaya Bello, ya bayyana tsohon Odita-Janar na Jihar Kogi,  Usman Ododo, a matsayin dan takararsa.

An gudanar da taron ne gabanin zaben dan takarar gwamnan jam’iyyar APC.

Baya ga Adodo da Onoja, sauran wadanda suka nuna sha’awar kujerar gwamnan sun hada da Mohammed Abdulkareem Asuku, ahugaban ma’aikatan Gwamna Yahaya Bello; tsohon kwamishina David Adebanji Jimoh; Asiwaju Ashiru Idris; da Okala Yakubu..

Sai dai majiyarmu a wurin taron ta ce dukkansu sun janye wa Adodo bayan gwamnan ya bayyana shi a matsayin zabinsa.

A wani sako da ya fitar Onoja ya bayyana goyon bayansa da godiya ga gwamnan, yana mai kira da jam’iyyar ta hada kai domin kaiwa ga nasara.

Shi na sakonsa, Asuku ya bayyana biyayyarsa ga matsayar da jam’iyyar ta dauka, tare da kira ga magoya bayansa su mara wa APC baya a zaben na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Wata majiya a jam’iyyar ta ce tun kafin Yahaya Bello ya bayyana zabinsa sauran masu zawarcin kujerar sun san cewa Ododo ne zabinsa.

Wani jigo a jam’iyyar ya ce Yahaya Bello ya sa sauran masu neman takarar su rubuta takardar janyewa, amma banda Ododon.

Wata majiya kuma ta ce an zabo Sanatan Kogi ta Gabas, Jibrin Isah, ya zama mataimakin Ododo, amma akwai shirye-shirye maye gurbinsa a nan gaba da Onoja.

Hakan zai kasance kamar abin da ya faru a Jihar Kaduna, inda Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe, ta janye takararta ta zama mataimakiyar Sanata Uba Sani.

Ko da yake shugaban kwamitin zaben, Gwamnan Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya ce sauran wadanda ke kan bakarsu na iya shiga a fafata da su a zaben dan takarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *