Kamfanin raba hasken wutar na kasa TCN, ya danganta rashin wutar lantarkin da ake fama da ita a jihar Kano sakamakon gazawar kamfanin wajen gyara wasu layukan tunkuda wutar, a daya daga cikin layin kamfanin mai karfin 330KVA da ke baiwa jihohin Kaduna da Kano, sakamakon ayyukan ‘yan bindiga a dajin Birnin Gwari.
Babban Manajan kamfanin TCN a yankin Kano Alh. Bashir Muhammad Gote a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, ya ce samun maatsalar da layukan suka yi, ya taimaka wajen shigar da jama’a da dama cikin wahala. Daily reporters24 ta rawaito.
A cewar kamfanin ayyukan ‘yan bindiga da suka mamaye dajin, ne ya sanya suka dauki lokaci wajen gyaran, kuma kamfanin na fargabar yiwuwar kai hari kan ma’aikatan da zasu yi aikin hakan ne ya sanya basu gyara ba.
Gote ya ce, “Muna fama da rashin wutar lantarki a Kano, sakamakon matsalar layin da ke samar da wutar lantarki zuwa Kaduna da Kano daga Dam din Shiroro.
“Babban kalubalen da ke gabanmu a halin yanzu shi ne yadda za mu yi sintiri a dajin Birning Gwari da ke Kaduna saboda fargabar ‘yan bindigar da suka boye a can suka taba kai hari kan ma’aikatanmu da jami’an tsaro da suka raka su a lokacin da muka samu irin wannan lamari a baya.
“Ina tabbatar muku cewa kamfanin na yin duk mai yiwuwa don gyara lamarin. Muna tsara dabarun yadda za a magance matsalar da kuma mayar da layin zuwa ga turakun,” in ji Gote.