Majalisa Ta Yi Sammacin Malami Da Zainab Ahmed Kan Zargin Badakalar $2.4bn

Kwamitin Majalsiar Wakilai da ke binciken zargin badakalar kudin man fetur har Dalar Amurka biliyan 2.3 ya yi sammacin Ministan Kudi, Kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed da na Shari’a, Abubakar Malami.

Kazalika, kwamitin ya kuma yi sammacin Sakataren Gwamnatin Tarayya da shi ma ya bayyana a gabanta a matsayin wani bangare na binciken da yake yi

Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah, ne ya bayar da sammacin lokacin da ya zauna ranar Talata.

Kwamitin dai na bincike ne kan zargin sayar da danyen mai kimanin ganga miliyan 48 ga kasar China da kudinsa ya kai Dalar biliyan biyu da miliyan 400 da aka yi harkallarsa daga 2014 zuwa yanzu.

Mark ya ce sun aike da sammacin ne da nufin sanin irin rawar da Ma’aikatar kudin da sauran hukumomin suka taka a zargin badakalar.

Ya ce, “Abin takaici ne cewa Ministan Shari’a da Ministar Kudi duk ba sa nan.

“Abin da muka bukata shi ne su bayyana a gaban kwamitin sabida mun aike musu da bukatar yin hakan a hukimance, saboda galibin abin da muke nema a ma’aikatunsu suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *