Maitaimakin sufeto-janar na ’yan sanda ya kai ziyara ga sarkin zazzau

Maitaimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Yemini Ayoku, ya kai ziyarar bankwana ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa.

Ziyarar ta zone saboda karin girma da ya samu daga matsayin Kwamishinan ’yan sanda zuwa Mataimakin Sufeto-Janar.

Kafin samun karin girman, Yekini shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna kuma yanzu haka an tura shi zuwa Hukumar Kula da Lafiyar Teku, domin ci gaba da aiki.

Mista Yekini ya bayyana godiya ga Masarautar Zazzau bisa hadin kai da goyon baya da ya samu a lokacin gudanar da aiki a matsayin kwamishinan ’yan sanda.

Ya kuma gode wa al’ummar Jihar Kaduna bisa taimaka masa da suka yi har ya sami nasara.

Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya taya Mista Yekini murna bisa karin girma da ya samu daga Kwamishina zuwa AIG.

Sarki Bamalli ya yi addu’ar samun ci gaba a duk inda aka sa gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *