NCC ta ce ba ita ce ke kula da abubuwan da ke cikin shafukan sada zumunta ba.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta ce ba ita ce ke kula da abubuwan da ke cikin shafukan sada zumunta ba.

Bayanin hakan ya fito ne a wata ziyara da kungiyar farar hula ta kasa (NCSCN) ta kai a baya bayan nan, karkashin jagorancin babban sakatarenta, Blessing Akinsolotu.

A yayin ziyarar ne ta nemi hukumar ta sa baki kan abubuwan da ke damun jama’a da yaudarar da tayi yawa a kafafen sada zumunta.

Akinlosotu ya ce lamarin ya bukaci masu ruwa da tsaki su gaggauta shiga tsakani don tabbatar da cewa abubuwan da ke cikin kafafen sada zumunta da na Intanet sun kasance masu inganci da kuma inganta hadin kan kasa.

Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Mista Reuben Muoka, wanda ya karbi bakuncin kungiyar a madadin Shugaban Hukumar, Farfesa Umar Danbatta, ya shaida wa kungiyar cewa aikin Hukumar bai shafi sarrafa abubuwan da ke cikin irin wadannan kafafen yada labarai ba.

A cewar Muoka, babban aikin hukumar kula da harkokin sadarwa shi ne saukaka tura sakonnin sadarwa da ke samar da nau’o’in ayyukan sadarwa daban-daban, ciki har da inganta hanyoyin sadarwa na zamani da ke kara kuzarin fasahar Intanet da tabbatar da gudanar da gasar gaskiya tare da kare masu amfani da wayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *