Gwamnatin tarayya ta kalubalanci Peter Obi dan takarar shugabancin kasar a zaben da ya gabata a karkashin jam’iyyar Labour, da ya fito ya fayyace matsayinsa dangane da sakon sautin da aka yada na tattaunawar da ta gudana tsakaninsa da shugaban babbar Mujami’ar ‘Living Faith’ Bishop David Oyedepo.
Ministan yada labaran Lai Mohammed ne ya kalubalanci Obi, yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin London.
A cewar Ministan, ya kamata dan takarar na Labour ya yi wa jama’a bayani kan abinda yake nufi da cewar, sautin da aka nadi muryarsa da ta Bishop na karya ne, wanda kuma aka yi amfani da wasu dabaru wajen samar da shi.
A farkon watan Afrilun nan, aka wayi gari da yaduwar sakon sautin da ke dauke da tattaunawar Peter Obi da Bishop Oyedepo, wanda cikinsa aka jiyo muryar dan takarar shugaban na Najeriya na neman taimakon Bishop din da ya ja hankalin mabiya addinin Kirista su goyi bayan takarar da yake yi, inda ya kuma bayyana zaben da ake tunkara a matsayin yaki na addini.
Sai dai daga baya Obi ya fito yayi watsi da sautin muryoyin, tare da bayyana shi a matsayin karyar da aka shirya domin bata masa suna.